عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ مَسْعُودٍ رضي الله عنه قَالَ: سَمِعْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«نَضَّرَ اللَّهُ امْرَأً سَمِعَ مِنَّا شَيْئًا فَبَلَّغَهُ كَمَا سَمِعَ، فَرُبَّ مُبَلِّغٍ أَوْعَى مِنْ سَامِعٍ».
[صحيح] - [رواه الترمذي وابن ماجه وأحمد] - [سنن الترمذي: 2657]
المزيــد ...
Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbbat a gare shi - yana cewa:
"Allah Ya ni'imtar da mutumin da ya ji wani abu daga gurimmu sai ya isar da shi kamar yadda ya ji, da yawa wanda aka isarwa yana zama mafi kiyayewa daga wanda ya ji".
[Ingantacce ne] - - [سنن الترمذي - 2657]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'a da ni'ima da farin ciki da kyau a duniya, kuma Allah Ya isar da shi zuwa ni'imar aljanna da ni'imarta a lahira; ga wanda ya ji zancensa sai ya haddace shi har ya isar da shi ga waninsa, sauda yawa wanda aka isarwa hadisin ya zama ya fi kiyayewa kuma ya fi fahimta kuma ya fi ikon yin istinbaɗi daga wanda ya ruwaito hadisin, sai na farkon ya zama yana kyautata hadda da dakkowa, na biyun kuma ya zama yana kyautata fahimta da istinbaɗi (tsamo hukunci).