عَنِ أبي زُهير عُمَارَةَ بْنِ رُؤَيْبَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم:
«لَنْ يَلِجَ النَّارَ أَحَدٌ صَلَّى قَبْلَ طُلُوعِ الشَّمْسِ وَقَبْلَ غُرُوبِهَا»
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 634]
المزيــد ...
Daga Abu Zauhair ɗan Ru'aibatu - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Duk wanda ya yi sallah kafin ɓullowar rana da kafin faɗuwarta ba zai shiga wuta ba".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 634]
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa: Babu wani ɗaya wanda ya sallaci sallar Asuba, da sallar La'asar kuma ya dawwama a kansu da zai shiga wuta; ya keɓanci waɗannan salloli biyun; domin cewa su ne mafi nauyin salloli, kuma cewa lokacin safiya yana kasancewa ne lokacin bacci da daɗinsa, lokacin La'asar kuma yana kasancewa ne a lokacin shagaltuwa da ayyukan yini da kuma kasuwancinsa, wanda ya kiyaye akan waɗannan salloli biyun tare da samun wahala to zai kiyaye akan ragowar sallolin.