+ -

عَنْ عُقْبَةَ بْنِ عَامِرٍ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«إِيَّاكُمْ وَالدُّخُولَ عَلَى النِّسَاءِ» فَقَالَ رَجُلٌ مِنَ الأَنْصَارِ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، أَفَرَأَيْتَ الحَمْوَ؟ قَالَ: «الحَمْوُ المَوْتُ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 5232]
المزيــد ...

Daga Uƙubah ɗan Amir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Na haneku da shiga wurin mata" sai wani mutum daga mutanen Madina ya ce: Ya Manzon Allah, shin kana ganin ƙanin miji fa? ya ce: "Ƙanin miji (shi ne) mutuwa".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 5232]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsoratar daga cakuɗuwa da mata ajanibai (waɗanda ba muharramai ba), ya ce: Ku kiyaye kawunanku da ku shiga gurin mata, mata kuma su shiga gurinku.
Sai wani mutum daga mutanen Madina ya ce: Shin kana ganin makusantan miji fa; kamar ɗan uwan miji da ɗan ɗan uwansa, da baffansa da ɗan baffansa, da ɗan 'yar uwarsa, da makamancinsu daga waɗanda aure da su yake halatta gare shi da a ce ba mai aure ba ce?
Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ku kiyaye shi kamar yadda kuke kiyayar mutuwa! domin kaɗaitaka da 'yan uwan miji mai kaiwa ne zuwa ga fitina da halaka a cikin Addini, makusantan miji banda iyayensa da 'ya'yansa sune mafi cancanta da hani cikin ajnabi; domin kaɗaitaka da makusancin miji tafi yawa daga kaɗaitaka da waninsa, kuma sharri ana tinanin afkuwarsa ne daga gare shi sama da waninsa ba tare da wani inakri akansa ba, kuma domin cewa shi babu makawa daga gare shi , kuma tsare shi ba ya yiwuwa daga gareta, yayin da al'ada ta gudana da sassauci a cikinsa sai namiji ya keɓanta da matar dan uwansa; to shi yana kama da mutuwa a muni da barna, sabanin namiji ajnabi cewa shi ana kulawa daga gare shi.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Swahili Yaran Tailand bushtu Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Oromo
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Hani daga shiga gun ajanibai da kaɗaitaka da su, dan toshe kafar afkawa cikin alfasha.
  2. Wannan mai gamewa ne a duk wani da ba mararrami ba na ɗan uwan miji da makusantansa, waɗanda su ba muharraman matar ba ne, kuma babu makawa da izina ta shigar ta zama mai kaiwa ce zuwa ga kaɗaitakarsu.
  3. Nisanta daga wuraren zamiya mai gamewane, dan tsoron afkawa cikin sharri.
  4. Al-Nawawi ya ce: Ma'abota ilimi na luga sun haɗu akan cewa al-Ahma'u (su ne) 'yan uwan mijin mace kamar babansa da baffansa, da ɗan uwansa da ɗan ɗan uwansa, da ɗan baffansa da makamancinsu, kuma al-Aktan (su ne) 'yan uwan matar mutum, surukai kuma sun haɗa nau'i biyun.
  5. Ya kamanta (ɗan uwan miji) da mutuwa, Ibnu Hajar ya ce; Larabawa suna siffanta abinda ake ƙi da mutuwa, ta fuskar kamanceceniyar cewa ita mutuwa ce a Addini idan saɓo ya afku, kuma mutuwar wacce aka keɓanta da ita ce idan saɓo ya afku kuma jifa ya wajaba, kuma halakar mace da rabuwar mijinta idan kishi ya ɗaike shi akan sakinta.