عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
أَنَّهُ كَانَ يَقُولُ إِذَا أَصْبَحَ: «اللهُمَّ بِكَ أَصْبَحْنَا، وَبِكَ أَمْسَيْنَا، وَبِكَ نَحْيَا، وَبِكَ نَمُوتُ، وَإِلَيْكَ النُّشُورُ» وَإِذَا أَمْسَى قَالَ: «بِكَ أَمْسَيْنَا، وَبِكَ أَصْبَحْنَا، وَبِكَ نَحْيَا، وَبِكَ نَمُوتُ، وَإِلَيْكَ النُّشُورُ» قَالَ: وَمَرَّةً أُخْرَى: «وَإِلَيْكَ الْمَصِيرُ».
[حسن] - [رواه أبو داود والترمذي والنسائي في الكبرى وابن ماجه] - [السنن الكبرى للنسائي: 10323]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -
Cewa shi ya kasance idan ya wayi gari yana cewa: "Ya Allah da (kiyayyewar) Ka ne muka wayi gari, kuma da (kiyayewar) Ka ne muka shiga maraice, da (al'amarin) Ka ne muka rayu, kuma da (al'amarin) Ka ne zamu mutu, kuma tashi (daga ƙabari) yana gareKa" Idan ya shiga maraice ya ce: "Da (kiyayewarka) Ka ne muka shiga maraice, kuma da (kiyayewar) Ka ne muka wayi gari, da (al'amarin) Ka zamu mutu, kuma tashi (daga ƙabari) yana gare Ka" ya ce: Wani lokaci kuma: "Makoma tana gare Ka".
[Hasan ne] - - [السنن الكبرى للنسائي - 10323]
(Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya kasance idan ya wayi gari shi ne farkon yini tare da ɓullowar alfijir yana cewa:
(Ya Allah da (kiyewar) Ka ne muka wayi gari) muna masu cakuɗuwa da kiyayewarKa ababen lulluɓewa da ni'imominKa, masu shagaltuwa da ambatanKa, masu neman taimako da sunanKa, masu tarowa da dacewarKa, masu motsawa da dabararKa da kuma ƙarfinKa, (da (kiyayewar) Ka ne muka shiga maraice, da (kiyayewar) Ka ne muka rayu, da (kiayewar) Ka ne zamu mutu) wato kamar lafazin da ya gabata tare da sanya shi a sama, sai ya ce: Ya Allah da Kai ne muka shiga maraice, kuma da sunanKa ne Mai rayawa muke rayuwa, da sunaKa ne Mai kashewa zamu mutu, (kuma gareKa ne tashi yake) da tashi bayan mutuwa, da rarrabuwa bayan haduwa, halinmu zai ci gaba akan haka a cikin dukkan lokuta, da ragowar halaye ba zan rabu ba daga gare shi kuma ba zan kaurace masa ba.
Idan ya shiga maraice bayan la'asar ya ce: "Ya Allah da (kiyayewar) Ka ne muka shiga maraice, kuma da (kiyayewar) Ka ne muka wayi gari, da (umarnin) Ka ne muke rayuwa, kuma (da al'amarin) Ka ne zamu mutu, makoma tana gare Ka) makoma a duniya, da makoma a ƙarshe, Kaine Kake rayani kuma kaine zaKa kasheni.