عَن أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«إِذَا تَثَاءَبَ أَحَدُكُمْ فَلْيُمْسِكْ بِيَدِهِ عَلَى فِيهِ، فَإِنَّ الشَّيْطَانَ يَدْخُلُ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2995]
المزيــد ...
Daga Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Idan ɗayanku zai yi hamma to ya riƙe bakainsa da hannunsa, domin cewa Shaiɗan yana shiga".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2995]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fadakar da wanda zai yi hamma cewa buɗe bakinsa saboda kasala ce ko cika ko wanin haka; cewa ya ɗora hannunsa akan bakinsa sai ya rufeshi da shi; hakan domin Shaiɗan yana shiga cikinsa idan ya barshi a buɗe, to ɗora hannu yana zama mai hana shigarsa.