عَنْ مَعْقِلِ بْنِ يَسَارٍ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«الْعِبَادَةُ فِي الْهَرْجِ كَهِجْرَةٍ إِلَيَّ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2948]
المزيــد ...
Daga Ma'ƙil ɗan Yasar - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Ibada a cikin rashin zaman lafiya kamar hijira ce zuwa gareni".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2948]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nunar zuwa ibada da yin riƙo da ita a cikin zamanin rashin zaman lafiya da fitina da yaƙe-yaƙe da cakuɗewar al'amuran mutane, kuma cewa ladanta kamar hijira ce zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, hakan domin cewa mutane suna rafkana daga gareta, suna shagaltuwa daga gareta, babu mai ƙoƙari gareta sai ɗaiɗaiku.