عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ:
أَنَّ أَعْرَابِيًّا أَتَى النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: دُلَّنِي عَلَى عَمَلٍ إِذَا عَمِلْتُهُ دَخَلْتُ الجَنَّةَ، قَالَ: «تَعْبُدُ اللَّهَ لاَ تُشْرِكُ بِهِ شَيْئًا، وَتُقِيمُ الصَّلاَةَ المَكْتُوبَةَ، وَتُؤَدِّي الزَّكَاةَ المَفْرُوضَةَ، وَتَصُومُ رَمَضَانَ» قَالَ: وَالَّذِي نَفْسِي بِيَدِهِ لاَ أَزِيدُ عَلَى هَذَا، فَلَمَّا وَلَّى قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ سَرَّهُ أَنْ يَنْظُرَ إِلَى رَجُلٍ مِنْ أَهْلِ الجَنَّةِ، فَلْيَنْظُرْ إِلَى هَذَا».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 1397]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -
Cewa wani balaraben kauye ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Ka shiryar da ni ga wani aiki wanda idan na yi shi, zan shiga aljanna, ya ce: "Ka bauta wa Allah, kada ka hada Shi da komai, ka tsayar da sallah, ka bayar da zakkar da aka wajabta, ka azimci Ramadan" Ya ce: Na rantse da Wanda raina yake a hannunSa, ba zan yi kari akan wannan ba, lokacin da ya juya ya tafi sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Wanda yake son ya kalli wani mutum daga 'yan aljanna, to ya yi duba zuwa ga wannan".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1397]
Wani mutum ya gabato daga mutanen kauye ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dan ya nuna masa aikin da zai shigar da shi aljanna, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya amsa masa da cewa shiga aljanna da tsira daga wuta sun tsaya akan bada rukunan Musulunci, na bautar Allah Shi kadai, kuma kada ka hada wani abu da Shi. Ka tsaida salloli biyar din Allah Ya wajabta su akan bayinSa a kowanne yini da dare. Ka bada zakkar dukiyar da Allah Ya wajabtasu akanka, ka bada su ga wadanda suka cancanta l. Ka kuma kiyaye akan azimin watan Ramadan a lokacinsa. Sai mutumin ya ce na rantse da wanda raina yake a hannunSa ba zan kara komai akan aikin da aka wajabta ba wanda na ji shi daga gareka na ayyukan da'a ba, kuma ba zan rage ba daga garesu ba. Lokacin da ya juya (ya tafi) sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Wanda yake son ya yi duba zuwa ga wani mutum daga 'yan aljanna to ya yi duba zuwa ga wannan balaraben kauyen.