عَنْ عَمْرِو بْنُ سُلَيْمٍ الأَنْصَارِيُّ قَالَ: أَشْهَدُ عَلَى أَبِي سَعِيدٍ قَالَ: أَشْهَدُ عَلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«الغُسْلُ يَوْمَ الجُمُعَةِ وَاجِبٌ عَلَى كُلِّ مُحْتَلِمٍ، وَأَنْ يَسْتَنَّ، وَأَنْ يَمَسَّ طِيبًا إِنْ وَجَدَ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 880]
المزيــد ...
Daga Amr Dan Sulaim Al-Ansari ya ce: Na shaida Abu sa'id ya ce: Na shaida Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Wanka ranar Juma'a wajibi ne akan kowanne baligi, kuma ya yi asuwaki, ya shafa tirare in ya samu".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 880]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanka ranar Juma'a abu ne mai karfi kamar wajibi a hakkin kowanne namiji baligi daga musulmai daga wanda juma'a ta wajaba akansa, kuma ya tsaftace hakoransa da asuwaki da makancinsa, ya kuma shafa tirare da kowanne irin tirare mai kanshi.