أَنَّ رَجُلًا سَأَلَ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: أَيُّ الإِسْلاَمِ خَيْرٌ؟ قَالَ: «تُطْعِمُ الطَّعَامَ، وَتَقْرَأُ السَّلاَمَ عَلَى مَنْ عَرَفْتَ وَمَنْ لَمْ تَعْرِفْ».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...
Cewa wani Mutum ya tambayi Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi: Wane aiki ne yafi a Musulunci? ya ce ka ciyar da Abinci kuma kayi Sallama ga wanda ka sani da wanda baka sani ba" .....
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Sahabbai sun tambaya wane aiki ne ya fi a Musulunci ya fi? ai ladaban Musulunci ko kuma halayen Ma'abotansa da suka fi lada ko suka fi yawan anfani? sai Annabi ya amsa da: Ciyar da Mutane Abinci, da yin Sallama ga Mutane ga wanda ka sani da wanda baka sani ba.