عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرٍو رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا:
أَنَّ رَجُلًا سَأَلَ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: أَيُّ الإِسْلاَمِ خَيْرٌ؟ قَالَ: «تُطْعِمُ الطَّعَامَ، وَتَقْرَأُ السَّلاَمَ عَلَى مَنْ عَرَفْتَ وَمَنْ لَمْ تَعْرِفْ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 12]
المزيــد ...
Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su -:
Cewa wani mutum ya tambayi Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi: Wanne aiki ne ya fi a Musulunci? ya ce: "Ka ciyar da abin ci, ka yi sallama ga wanda ka sani da wanda baka sani ba".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 12]
An tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wadanne dabi'u ne na Musulunci suka fi? sai ya ambaci dabi'u biyu:
Na farko: Yawaita ciyar da abin ci ga talakawa, sadaka da kyauta da saukar bako da walima za su shiga ciki, falalar ciyarwa tana karfafa alokutan yunwa da tsadar farashi.
na biyu: Yin sallama ga kowanne musulmi, ka san shi ko ba ka san shi ba.