عن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما مرفوعاً: «الْحَيَاء مِنْ الْإِيمَانِ».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...
Daga Abdullahi Bn Umar -Allah ya yarda da su- zuwa ga Annabi "Kunya tana daga cikion Imani"
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
Jin kunya daga imani ne, saboda mai jin kunya yana dauke jin kunyarsa daga zunubai kuma ya cika ayyuka, wannan kuwa yana daga tasirin imani da Allah - Madaukaki - idan ta cika zuciya da ita, tana hana mai ita daga zunubai kuma tana kwadaitar da shi ya aiwatar da ayyukan, don haka kunya ta zama kamar imani, dangane da tasirin fa'idanta ga bawa.