عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بنِ مسعُودٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ:
ذُكِرَ عِنْدَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَجُلٌ نَامَ لَيْلَهُ حَتَّى أَصْبَحَ، قَالَ: «ذَاكَ رَجُلٌ بَالَ الشَّيْطَانُ فِي أُذُنَيْهِ، أَوْ قَالَ: فِي أُذُنِهِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 3270]
المزيــد ...
Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
An anbaci wani mutum da ya yi bacci a darensa har saida ya wayi gari a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya ce: "Wancan wani mutum ne wanda Shaiɗan ya yi fitsari a cikin kunnuwansa, ko ce ya yi: A cikin kunnensa".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 3270]
An anbaci wani mutumin da ya yi bacci har gari ya waye rana ta ɓullo bai tashi ya yi sallar farilla ba a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai shi wani mutum ne wanda Shaiɗan ya yi fitsari a cikin kunnansa.