عَن أَبِي أُمَامَةَ قَالَ: حَدَّثَنِي عَمْرُو بْنُ عَبَسَةَ رضي الله عنه أَنَّهُ سَمِعَ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«أَقْرَبُ مَا يَكُونُ الرَّبُّ مِنَ العَبْدِ فِي جَوْفِ اللَّيْلِ الآخِرِ، فَإِنْ اسْتَطَعْتَ أَنْ تَكُونَ مِمَّنْ يَذْكُرُ اللَّهَ فِي تِلْكَ السَّاعَةِ فَكُنْ».
[صحيح] - [رواه أبو داود والترمذي والنسائي] - [سنن الترمذي: 3579]
المزيــد ...
Daga Abu Umamah ya ce: Amr ɗan Abasa - Allah Ya yarda da shi - ya zantar da ni cewa shi ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
"Mafi kusancin lokacin da bawa yake kasancewa kusa da Ubangiji a cikin (kason) dare na karshe, idan kana da ikon ka kasance daga wanda yake ambatan Allah a wannan lokacin to ka kasance".
[Ingantacce ne] - - [سنن الترمذي - 3579]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Ubangiji - tsarki ya tabbatar maSa - Shi ne mafi kusa ga bawa a lokacin sulusin dare na karshe; idan an datar da kai kuma ka samu iko - ya kai mumini - da ka kasance daga jumlar masu bauta masu sallah masu ambatan Allah masu tuba a wannan lokacin to shi wani al'amari ne wanda yana kamata a ci ribarsa da kokari a cikinsa.