1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana yawaita faɗin: "Ya mai jujjuya zukata Ka tabbatar da zuciyata akan addininKa

عَنْ أَنَسٍ رضي الله عنه قَالَ:
كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُكْثِرُ أَنْ يَقُولَ: «يَا مُقَلِّبَ القُلُوبِ ثَبِّتْ قَلْبِي عَلَى دِينِكَ»، فَقُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ، آمَنَّا بِكَ وَبِمَا جِئْتَ بِهِ فَهَلْ تَخَافُ عَلَيْنَا؟ قَالَ: «نَعَمْ، إِنَّ القُلُوبَ بَيْنَ أُصْبُعَيْنِ مِنْ أَصَابِعِ اللهِ يُقَلِّبُهَا كَيْفَ يَشَاءُ».

Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana yawaita faɗin: "Ya mai jujjuya zukata Ka tabbatar da zuciyata akan addininKa" sai na ce: Ya Manzon Allah, mun yi imani da kai da kuma abinda ka zo da shi, shin kana jin tsoro akanmu ne? ya ce: "Eh, lallai zukata suna tsakanin yatsu biyu daga yatsun Allah Yana jujjuyasu yadda Ya ga dama".

Ingantacce ne Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi Sunan Tirmizi - 2140

Bayani

Mafi yawan addu'ar Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance rokon Allah ne tabbata akan addini da biyayya, da nisanta daga karkata da kuma bata, Sai Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya yi mamakin yawaitawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan wannan addu'ar, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ba shi labarin cewa zukata suna tsakanin yatsu biyu daga yatsun Allah Yana juyasu yadda Ya ga dama, Zuciya ita ce gurin imani da kafirci, hakika an anbaci zuciya (Kalbu) saboda yawan jujjuawarta; ita ce mafi tsananin jujjuyawa daga tukunya idan ta tafarfasa, wanda Allah Ya so Zai tsaida zuciyarsa akan shiriya, ya tabbatar da shi akan addini, wanda Allah Ya ga dama kuma Zai juyar da zuciyarsa daga shiriya zuwa karkata da bata.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kankan da kan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga Ubangijinsa da kankar dakai gareShi, da nunawa al'umma rokon hakan.
  2. Muhimmancin tsayuwa akan gaskiya da tabbata akan addini, kuma izina da karshe ne.
  3. Bawa ba ya wadatuwa daga Allah Ya tabbatarwa shi akan musulunci koda kiftawar ido.
  4. Kwadaitarwa akan yawaita wannan addu'ar dan koyi da Annabi - tsira da aminci su tabbata agare shi -.
  5. Tabbata akan musulunci shi ne ni'ima mafi girma wacce yake kamata ga bawa ya yi kokari gareta kuma ya godewa Ubangijinsa akanta.

Manufofin Fassarorin

53 Yare
EN English الإنجليزية
UR اردو الأوردية
ES Español الإسبانية
ID Indonesia الإندونيسية
UG ئۇيغۇرچە الأيغورية
BN বাংলা البنغالية
TR Türkçe التركية
RU Русский الروسية
BS Bosanski البوسنية
SI සිංහල السنهالية
HI हिन्दी الهندية
ZH 中文 الصينية
FA فارسی الفارسية
VI Tiếng Việt الفيتنامية
TL Tagalog تجالوج
KU Kurdî الكردية
PT Português البرتغالية
ML മലയാളം المليالم
TE తెలుగు التلغو
SW Kiswahili السواحيلية
TA தமிழ் التاميلية
MY မြန်မာ البورمية
TH ไทย التايلندية
DE Deutsch الألمانية
PS پښتو بشتو
AS অসমীয়া الأسامية
SQ Shqip الألبانية
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча القيرقيزية
NE नेपाली النيبالية
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda الكينياروندا
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy المالاجاشية
OM Oromoo الأورومو
KN ಕನ್ನಡ الكانادا
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan الأذربيجانية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية