+ -

عَنْ سَعْدٍ رضي الله عنها قَالَ:
جَاءَ أَعْرَابِيٌّ إِلَى رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: عَلِّمْنِي كَلَامًا أَقُولُهُ، قَالَ: «قُلْ: لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، اللهُ أَكْبَرُ كَبِيرًا، وَالْحَمْدُ لِلَّهِ كَثِيرًا، سُبْحَانَ اللهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ، لَا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللهِ الْعَزِيزِ الْحَكِيمِ» قَالَ: فَهَؤُلَاءِ لِرَبِّي، فَمَا لِي؟ قَالَ: «قُلْ: اللهُمَّ اغْفِرْ لِي وَارْحَمْنِي وَاهْدِنِي وَارْزُقْنِي».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2696]
المزيــد ...

Daga Sa'ad - Allah Ya yarda da su - ya ce:
Wani balaraben kauye ya zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Ka sanar maganar da zan fada, ya ce: "Ka ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai Yake ba Shi da abokin tarayya, Allah ne Mafi girma Mai girma, godiya ta tabbata ga Allah mai yawa, tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai, babu dabara babu karfi sai ga Allah Mabuwayi Gwani" sai ya ce: Wadannan na Ubangijina ne, to ni me gareni? ya ce: "Ka ce: Ya Allah Ka gafarta mini Ka ji kaina Ka shiryar dani Ka azurtani".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2696]

Bayani

Wani mutum daga mazauna kauye ya tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar da shi wani zikirin da zai fade shi, Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ka ce: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai yake ba da abokin tarayya" ya fara da shahada ta tauhidi, ma'anarta babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, "Allah ne Mafi girma Mai girma" Wato: Allah ne Mafi girma daga kowanne abu kuma Mafi girma, "Godiya ta tabbata ga Allah mai yawa" Wato: Godiya ta tabbata ga Allah mai yawa, ga siffofinSa da ayyukanSa da ni'imominSa wadanda ba'a iya lissafe su, "Tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai" Wato: Ya tsarkaka Ya tsarkaka daga tawaya, "Babu dabara babu karfi sai ga Allah Ubangiji Mabuwayi Gwani" Wato: Babu dabara ta canza wa daga wani hali zuwa wani halin sai ga Allah da taimakonSa da gamkatar dinSa, sai mutumin ya ce: Wadannan kalmomin sun tabbata ga Ubanigijina dan ambatonSa da girmamaShi, to ni meye gareni na addu'a ga kaina? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ka ce: "Ya Allah Ka gafarta mini" Da shafe munanan ayyuka da suturta su, "Ka jikaina" Ta hanyar sadar da abubuwan amfani da maslahohi na Addini da duniya gareni, "Ka shiryr da ni" ga mafi kyawun halaye kuma zuwa ga hanya mikakkiya, "Ka azirtani" Dukiya ta halal da lafiya da dukkanin alheri da lafiya.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية التشيكية Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwadaitarwa akan anbaton Allah da hailala da kabbara da tahmidi da tasbihi.
  2. An so anbaton Allah da yabo gareShi kafin fara addu'a.
  3. Anso addu'ar mutum da mafi tsarkakan addu'o'i, da kuma abinda aka ciro wanda a cikinsa akwai tattaro alherin duniya da lahira. Kuma yana da damar addu'a da abinda ya so.
  4. Yana kamata ga bawa ya yi kwadayi akan neman ilimin abinda zai amfanar da shi a duniya da lahira.
  5. Kwadaitarwa akan neman gafara da rahama da arziki, su ne matattarar alheri.
  6. Tausayinsa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi akan ilmantar da al'ummarsa abinda zai amfanar da su.
  7. An ambaci rahama bayan gafara dan tsarkakewa ta cika, gafara ita ce suturta zunubai da shafesu da nisanta daga wuta, rahama kuwa ita ce sadar da alherai da shiga aljanna, wannan shi ne rabo mai girma.