+ -

عَنْ أَبَي قَتَادَةَ رضي الله عنه أنَّهُ طَلَبَ غَرِيمًا لَهُ، فَتَوَارَى عَنْهُ ثُمَّ وَجَدَهُ، فَقَالَ: إِنِّي مُعْسِرٌ، فَقَالَ: آللَّهِ؟ قَالَ: آللَّهِ؟ قَالَ: فَإِنِّي سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«مَنْ سَرَّهُ أَنْ يُنْجِيَهُ اللهُ مِنْ كُرَبِ يَوْمِ الْقِيَامَةِ فَلْيُنَفِّسْ عَنْ مُعْسِرٍ أَوْ يَضَعْ عَنْهُ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 1563]
المزيــد ...

Daga Abu Katada - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya nemi wani wanda yake bin sa bashi, sai ya ɓuya daga gare shi, sai ya ce: Lallai ni bani da kuɗi, sai ya ce: (tskaninka da) Allah? ya ce: (tsakanina da) Allah? ya ce: Lallai ni naji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
"Wanda yake son Allah Ya tseratar da shi daga baƙin cikin ranar Alƙiyama, to, ya yaye wa wanda yake cikin wani mawuyacin hali, ko ya sarayar masa (wani haƙƙi ko nauyin da ya ke kansa)".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1563]

Bayani

Abu Katadah alAnsari - Allah Ya yarda da shi - ya kasance yana binciken wani wanda yake binsa bashi wanda yake ɓoye masa, sai ya same shi, sai wanda ake bi bashi ya ce: Lallai ni bani da kuɗi, kuma bani da dukiyar da zan biya bashinka.
Sai Abu Katadah - Allah Ya yarda da shi - ya sa ya rantse da Allah cewa shi bashi da dukiya?
Sai ya rantse da Allah cewa shi mai gaskiya a abinda yake faɗa.
Sai Abu Katadah - Allah Ya yarda da shi - ya ce lallai shi ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
Wanda yake so kuma yake farin ciki Allah Ya tseratar da shi daga baƙin cikin ranar alƙiyama da tsanace-tsanancanta da tsorace-tsoracenta, to ya yayewa wanda yake cikin ƙunci, shi ne cewa ya ƙara (lokaci) ya jinkirta neman bashin, ko ya sarayar da sashin bashin ko ma dukkansa.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Yaran Tailand bushtu Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية النيبالية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. An so saurarawa wanda ke cikin ƙunci zuwa lokacin samun walwala, ko sarayar da bashin daga gare shi gaba ɗayansa ko sashinsa.
  2. wanda ya yayewa mumini baƙin cikin duniya Allah Zai yaye masa baƙin cikin ranar alƙiyama, sakamako yana daga jinsin aiki.
  3. Ka'ida (ita ce): Lallai cewa farillai sun fi nafilfili, sai dai a wasu lokuta nafila tana zama ta fi farilla, sarayar da bashi daga wanda ke cikin ƙunci nafila ne, kuma yi masa haƙuri da saurare da rashin neman to wannan farilla ne, nafila ta fi farilla a nan.
  4. Hadisin yana (bayani) a cikin haƙƙin wanda ke cikin ƙunci, to wannan an yi masa uzuri, amma mai taurin bashi wanda yana da dukiya, to haƙiƙa ya zo daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya ce: "Taurin bashin mawadaci zalinci ne".