1. Gida
  2. kashe kashe

Sabuntawa Akan me zamu yi maka caffa? ya ce: "Akan ku bautawa Allah kuma kada ku sanya wa Allah wani abun tarayya da Shi, da salloli biyar, ku bi - sai ya boye wata kalma boyayya - kada ku tambayi mutane komai

عَنْ أَبِي مُسْلِمٍ الْخَوْلَانِيِّ، قَالَ: حَدَّثَنِي الْحَبِيبُ الْأَمِينُ، أَمَّا هُوَ فَحَبِيبٌ إِلَيَّ، وَأَمَّا هُوَ عِنْدِي فَأَمِينٌ، عَوْفُ بْنُ مَالِكٍ الْأَشْجَعِيُّ رضي الله عنه قَالَ:

كُنَّا عِنْدَ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، تِسْعَةً أَوْ ثَمَانِيَةً أَوْ سَبْعَةً، فَقَالَ: «أَلَا تُبَايِعُونَ رَسُولَ اللهِ؟» وَكُنَّا حَدِيثَ عَهْدٍ بِبَيْعَةٍ، فَقُلْنَا: قَدْ بَايَعْنَاكَ يَا رَسُولَ اللهِ، ثُمَّ قَالَ: «أَلَا تُبَايِعُونَ رَسُولَ اللهِ؟» فَقُلْنَا: قَدْ بَايَعْنَاكَ يَا رَسُولَ اللهِ، ثُمَّ قَالَ: «أَلَا تُبَايِعُونَ رَسُولَ اللهِ؟» قَالَ: فَبَسَطْنَا أَيْدِيَنَا وَقُلْنَا: قَدْ بَايَعْنَاكَ يَا رَسُولَ اللهِ، فَعَلَامَ نُبَايِعُكَ؟ قَالَ: «عَلَى أَنْ تَعْبُدُوا اللهَ وَلَا تُشْرِكُوا بِهِ شَيْئًا، وَالصَّلَوَاتِ الْخَمْسِ، وَتُطِيعُوا -وَأَسَرَّ كَلِمَةً خَفِيَّةً- وَلَا تَسْأَلُوا النَّاسَ شَيْئًا» فَلَقَدْ رَأَيْتُ بَعْضَ أُولَئِكَ النَّفَرِ يَسْقُطُ سَوْطُ أَحَدِهِمْ، فَمَا يَسْأَلُ أَحَدًا يُنَاوِلُهُ إِيَّاهُ.

Daga Abu Muslim Al-Khaulani ya ce: Masoyi amintacce ya zantar dani, amma shi to masoyi ne gareni, amma shi a wajena to amintaccene, Awf Dan Malik Al-Ashja'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Mun kasance wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - (Mu) tara ko takwas ko bakwai, sai ya ce: "Shin ba kwa yi wa Manzon Allah caffa ba?" mun kasance farkon yin caffa (mubaya’a) sai muka ce: Hakika mun yi maka caffa ya Manzon Allah, sannan ya ce: "Shin bakwa yi wa Manzon Allah caffa ba?" sai muka ce: Hakika mun yi maka caffa ya Manzon Allah, sannan Ya ce: "Shin bakwa wa Manzon Allah caffa ba?" Ya ce: Sai muka shimfida hannayenmu muka ce: Hakika mun yi maka caffa ya Manzon Allah, Akan me zamu yi maka caffa? ya ce: "Akan ku bautawa Allah kuma kada ku sanya wa Allah wani abun tarayya da Shi, da salloli biyar, ku bi - sai ya boye wata kalma boyayya - kada ku tambayi mutane komai" Hakika na ga sashin wadancan mutanan bulalar dayansu tana faduwa, amma ba ya tambayar wani ya miko masa.

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 1043

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance a cikin wani adadi na sahabbai sai ya nemi su yi masa caffa su yi masa alkawari akan lazimtar wasu al'amura har sau uku:
Na farko: Bautar Allah Shi kadai ta hanyar riko da umarninSa, da nisantar haninSa, kuma kada su hada wani abu daShi.
Na biyu: Tsaida salloli biyar na wajibai a yini da dare.
Na uku: Ji da bi da aikin alheri ga wanda ya jibinci al'amarin musulmai.
Na hudu: Kai dukkanin bukatunsu ga Allah da rashin tambayar mutane wani abu daga garesu, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi kasa-kasa da sautinsa da su.
Hakika sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun yi aiki da abinda suka yi caffa akansa, har maruwaicin Hadisin ya ce: Hakika na ga wasu daga wadancan sahabban bulalar dayansu tana faduwa kasa , amma ba ya tambayar wani ya miko masa ita, kai yana sauka yana daukarta da kansa.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwadaitarwa akan barin tambayar mutane, da tsarkaka daga dukkanin abinda ake kira tambaya, da wadatuwa daga mutane koda a wani al'amari kankani ne.
  2. Tambayar da aka hana: Tambaya mai alaka da al'amura na duniya, ba ta hado tambaya game da ilimi da al'amuran Addini ba.

Manufofin Fassarorin

58 Yare
EN English الإنجليزية
UR اردو الأوردية
ES Español الإسبانية
ID Indonesia الإندونيسية
UG ئۇيغۇرچە الأيغورية
BN বাংলা البنغالية
FR Français الفرنسية
TR Türkçe التركية
RU Русский الروسية
BS Bosanski البوسنية
SI සිංහල السنهالية
HI हिन्दी الهندية
ZH 中文 الصينية
FA فارسی الفارسية
VI Tiếng Việt الفيتنامية
TL Tagalog تجالوج
KU Kurdî الكردية
PT Português البرتغالية
ML മലയാളം المليالم
TE తెలుగు التلغو
SW Kiswahili السواحيلية
MY မြန်မာ البورمية
TH ไทย التايلندية
DE Deutsch الألمانية
PS پښتو بشتو
AS অসমীয়া الأسامية
SQ Shqip الألبانية
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча القيرقيزية
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá اليوروبا
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda الكينياروندا
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy المالاجاشية
IT Italiano الإيطالية
OM Oromoo الأورومو
KN ಕನ್ನಡ الكانادا
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan الأذربيجانية
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
KMR Kurmancî الكرمنجية
kashe kashe
  • . .