عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«إِذَا انْتَهَى أَحَدُكُمْ إِلَى الْمَجْلِسِ فَلْيُسَلِّمْ، فَإِذَا أَرَادَ أَنْ يَقُومَ فَلْيُسَلِّمْ، فَلَيْسَتِ الْأُولَى بِأَحَقَّ مِنَ الْآخِرَةِ».
[حسن] - [رواه أبو داود والترمذي والنسائي في الكبرى وأحمد] - [سنن أبي داود: 5208]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Idan ɗayanku ya isa zuwa ga majalisa to ya yi sallama, idan kuma yana so ya tashi to ya yi sallama, domin (sallama) ta farkon bata fi mafi cancanta daga ta ƙarshe ba".
[Hasan ne] - [Al-Nasa'i Ya Rawaito shi] - [سنن أبي داود - 5208]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da wanda ya zo wurin zaman mutane da ya yi musu sallama, idan kuma ya yi nufin ya tashi daga wurin to ya yi wa mutanen wurin bankwana da yin sallama; dan sallamar farkon lokacin zuwa ba ta fi mafi cancanta daga ɗayar sallamar a lokacin da zai bar wurinba.