عَن عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما قَالَ: سُئِلَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنِ الْمَاءِ وَمَا يَنُوبُهُ مِنَ الدَّوَابِّ وَالسِّبَاعِ، فَقَالَ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«إِذَا كَانَ الْمَاءُ قُلَّتَيْنِ لَمْ يَحْمِلِ الْخَبَثَ».
[صحيح] - [رواه أبو داود والترمذي والنسائي وابن ماجه وأحمد] - [سنن أبي داود: 63]
المزيــد ...
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: An tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da ruwa da abinda yake zuwa masa na dabbobi da zakokai, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce:
"Idan ruwa ya zama tulu biyu baya ɗaukar najasa".
[Ingantacce ne] - - [سنن أبي داود - 63]
An tamnayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da hukuncin tsarkin ruwa wanda dabbobi da zakokai suke zuwa domin su sha da makancinsa, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ruwa idan awonsa yakai manyan tulu biyu, su sun yi daidai da: Lita (210) cewa shi ruwa ne mai yawa ba ya najastuwa; sai dai idan ɗayan siffofinsa uku ya canja da najasa (su ne) launinsa ko ɗanɗanonsa ko warinsa.