عن أبي هريرة رضي الله عنه مرفوعاً: "لا يَبُولَنَّ أحَدُكم في الماء الدَّائِم الذي لا يجْرِي، ثمَّ يَغتَسِل مِنه". وفي رواية: "لا يغتسل أحدكُم في الماء الدَّائم وهو جُنُب".
[صحيح] - [الرواية الأولى: متفق عليها. الرواية الثانية: رواها مسلم]
المزيــد ...

An karbo daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - an daga shi zuwa g Annabi: 'kar waninku ya yi fitsari a cikin ruwan da ba ya gudana, sannan ya yi wanka da shi" A wata ruwayar: 'kar waninku ya yi wanka da ruwan da ba ya gudan alhali yana da janaba"
Ingantacce ne - Muslim ne ya rawaito shi

Bayani

Annabi mai tsira d a aminci ya yi hani ga yin fitsari a cikin ruwan da ba ya gudana, saboda hakan ka iya janyo cakuduwarsa da najasa da cututtukan da fitsarin ke dauke da su, wanda sa iya cutar da wanda ya yi amfani da su, ta iya yiwuwa mai yin fitsarinma da kanshi zai iya yin wanka da shi. to ta yaya zai yi fitsari cikin abin da zai iya zama abin tsarkinsa. Hakanan kuma ya yi hani ga yin wankan janaba a cikin ruwan da ba ya gudana; saboda yin hakan zai iya bata ruwan da datti da kazantar janaba.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Uighur Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin