عن عبد الله بن عباس رضي الله عنهما قال: اغتسل بعض أزواج النبي صلى الله عليه وسلم في جَفْنَةٍ، فجاء النبي صلى الله عليه وسلم ليتوضأ منها أو يغتسل، فقالت: له يا رسول الله، إني كنت جُنُبًا؟ فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «إن الماء لا يَجْنُبُ».
[صحيح] - [رواه أبو داود والترمذي وابن ماجه]
المزيــد ...

Wannan fassarar tana bukatar Karin bita da gyaran yare.

An karvo daga Abdullahi Bn Abbas -Allah ya yarda da su- ya ce: wasu daga cikin Matan Annabi SAW sunyi Wanka a cikin Daro, sai Manzon Allah ya zo zai yi Al-wala daga ciki ko zai yi wanka, sai ta ce da shi: Ya manzon Allah nifa na kasance ina da janaba? sai Manzon Allah SAW ya ce: "Lallai ruwa baya yin Najasa"
Ingantacce ne - Ibnu Majah ne ya Rawaito shi

Bayani

Xaya daga cikin Matan Manzon Allah SAW tayi Wankan Janaba, sai Manzon Allah SAW yazo zaiyi Al-wala ko wanka; sai yaso yayi amfani da ruwan da ya ragu na ruwan Wankan Matarsa -Allah ya yarda da ita- sai ta gaya masa cewa ita ta kasance tana da Janaba, sai ya nusar da ita cewa hakan ba zaiyi tasiri a ruwan ba, kasancewar sa mai tsarki kuma abun tsarkakewa

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa
Manufofin Fassarorin
Kari