عَنْ أُبَيِّ بْنِ كَعْبٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«يَا أَبَا الْمُنْذِرِ، أَتَدْرِي أَيُّ آيَةٍ مِنْ كِتَابِ اللهِ مَعَكَ أَعْظَمُ؟» قَالَ: قُلْتُ: اللهُ وَرَسُولُهُ أَعْلَمُ. قَالَ: «يَا أَبَا الْمُنْذِرِ، أَتَدْرِي أَيُّ آيَةٍ مِنْ كِتَابِ اللهِ مَعَكَ أَعْظَمُ؟» قَالَ: قُلْتُ: {اللهُ لا إِلَهَ إِلا هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ} [البقرة: 255]. قَالَ: فَضَرَبَ فِي صَدْرِي، وَقَالَ: «وَاللهِ لِيَهْنِكَ الْعِلْمُ، أَبَا الْمُنْذِرِ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 810]
المزيــد ...
Daga Ubayyu Dan Ka'ab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Ya kai baban Munzir, shin ka san wacce aya ce daga littafin Allah mafi girma tare da kai?" ya ce: Na ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani. Ya ce: "Yakai baban Al-Munzir, shin ka san wacce aya ce daga littafin Allah mafi girma tare dakai?" ya ce: Na ce; {Allah wanda babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi Rayayye Tabbatacce da kanSa} [Al-Baqara: 255]. Ya ce: Sai ya daki kirjina, ya ce: "Wallahi ilimi ya faranta maka kai baban Al-Munzir".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 810]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi Ubayyu Dan Ka'ab game da mafi girman aya a cikin littafin Allah, sai ya yi kai kawo a amsa, sannan ya ce: ita ce Ayatul Kursiyyi: {Allah babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi, Rayayye tabbatacce da kanSa}, sai Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karfafashi, kuma Annabi ya daki kirjinsa dan nuni zuwa cikarsa da ilimi da hikima, kuma ya yi masa addu'a da ya tsira da wannan ilimin kuma ya sawwaka masa shi.