عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«مَنْ عَادَ مَرِيضًا، لَمْ يَحْضُرْ أَجَلُهُ فَقَالَ عِنْدَهُ سَبْعَ مِرَارٍ: أَسْأَلُ اللَّهَ الْعَظِيمَ رَبَّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ أَنْ يَشْفِيَكَ، إِلَّا عَافَاهُ اللَّهُ مِنْ ذَلِكَ الْمَرَضِ».
[صحيح] - [رواه أبو داود والترمذي وأحمد] - [سنن أبي داود: 3106]
المزيــد ...
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya duba mara lafiya (wanda) ajalinsa bai yi ba, sai ya ce a wurinsa sau bakwai: Ina roƙon Allah Mai girma Ubangijin al-Arshi Mai girma Ya baka lafiya, sai Allah Ya ba shi lafiya daga wannan cutar".
[Ingantacce ne] - - [سنن أبي داود - 3106]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wani musulmin da zai ziyarci wani musulmi a cikin rashin lafiyarsa wanda lokacin mutuwarsa bai yi ba, sannan mai ziyarar ya yi wa mara lafiya addu'a da faɗinsa: (Ina roƙon Allah Mai girma) a cikin zatinSa da siffofinSa da ayyukanSa, (Ubangijin al-Arshi Mai girma Ya baka lafiya), kuma ya maimaitata hakan sau bakwai sai Allah Ya ba shi lafiya daga wannan cutar.