عَنْ عَلِيٍّ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ لِي رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«قُلِ اللهُمَّ اهْدِنِي وَسَدِّدْنِي، وَاذْكُرْ بِالْهُدَى هِدَايَتَكَ الطَّرِيقَ، وَالسَّدَادِ سَدَادَ السَّهْمِ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2725]
المزيــد ...
Daga Ali - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce da ni:
"ka ce Ya Allah Ka shiryar dani Ka datar dani, ka ambaci shiriya (irin) shiriyarka ta hanya, da dacewa (irin) dacewar kibiya
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2725]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci Ali ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya roƙi Allah ya tambaye shi sai ya ce: (Ya Allah Ka shiryar da ni) Ka shiryar da ni Ka nuna mini (Ka datar da ni) Ka yi mini gam da katar, Ka sanya ni madaidaici a dukkan al'amurana.
Shiriya: Ita ce sanin gaskiya a fayyace kuma a dunƙule, da dacewa ga binta a zahiri da baɗini.
Dacewa kuwa: Ita ce dacewa da daidaita a dukkanin al'amura da abinda zai zama daidai akan gaskiya, shi ne hanya madaidaiciya a magana da aiki da ƙudiri.
Kuma cewa umarni na ma'ana yana bayyana da abin ji; ka tina alhali kai kana yin wannan addu'ar cewa: (Shiriya: Shiriyarka (irin ta) hanya) ka halarto zuciyarka alhali kai kana roƙon shiriya kamar shiriyar wanda ya yi tafiya, cewa shi baya kaucewa akan hanya dama da hagu; hakan dan ya kuɓuta daga ɓata (makuwa), da haka ne zai samu kuɓuta, ya kai zuwa manufarsa a gaggauce.
(Daidaita: (irin) daidaitar kibiya) kai kana lura a lokacin da kake daidaita kibiya a gaggawar saduwarta da samunta ga inda aka harbata, mai harbi idan ya harbi inda yake so sai ya daidaita kibiya wajen inda zai harba, to haka nan zaka roƙi Allah - Maɗaukakin sarki - cewa abinda ka yi niyyarsa na daidai yana kan yanayin kibiya; sai ka zama a roƙonka mai neman matuƙar shiriya, da ƙarshen daidaita.
Ka halarto wannan ma'anar a zuciyarka har sai ka roƙi Allah daidai dan abinda ka yi niyyarsa daga hakan ya zama akan yanayin abinda kake anfani da shi na harbi.