عَنْ عُبَيْدِ اللَّهِ بْنِ مِحْصَنٍ الْأَنْصَارِيِّ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«مَنْ أَصْبَحَ مِنْكُمْ مُعَافى فِي جَسَدِهِ، آمِنًا فِي سِرْبِهِ، عِنْدَهُ قُوتُ يَوْمِهِ، فَكَأَنَّمَا حِيزَتْ لَهُ الدُّنْيَا».
[حسن] - [رواه الترمذي وابن ماجه] - [سنن ابن ماجه: 4141]
المزيــد ...
Daga Ubaidullahi ɗan Mihsan al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Wanda ya wayi gari daga cikinku lafiyayye a cikin jikinsa, kuma amintacce a cikin jama'arsa (ko ransa), kuma yana da abin cin yininsa, to kamar an tattaro masa duniya ne».
[Hasan ne] - - [سنن ابن ماجه - 4141]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa yaku musulmai duk wanda ya wayi gari a cikinku yana mai lafiyayye kuɓutacce a cikin jikinsa daga illoli da cututtuka, kuma yana amintacce a cikin ransa da iyalansa da hanyarsa ba ya tsoro, kuma yana da isasshen abin cin yininsa na halal; to kamar an tattara masa duniya ne gabaɗayanta.