Karkasawa: Falaloli da Ladabai .
+ -

عَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللهِ رضي الله عنهما أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«اتَّقُوا الظُّلْمَ، فَإِنَّ الظُّلْمَ ظُلُمَاتٌ يَوْمَ الْقِيَامَةِ، وَاتَّقُوا الشُّحَّ، فَإِنَّ الشُّحَّ أَهْلَكَ مَنْ كَانَ قَبْلَكُمْ، حَمَلَهُمْ عَلَى أَنْ سَفَكُوا دِمَاءَهُمْ وَاسْتَحَلُّوا مَحَارِمَهُمْ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2578]
المزيــد ...

Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Ku ji tsoron zalunci, domin zalunci duhu ne ranar Alkiyama, Ku ji tsoron kwauro, domin kwauro shi ne ya hallaka wadanda suka gabaceku, har ya kaisu sun zubar da jininsu, suka halarta abinda aka haramta musu".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2578]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargadi daga zalinci. Daga cikin Nau’ukansa akwai: Zalintar mutane da zalintar kai, da zalinci a hakkin Allah - Madakakin sarki -, Shi ne kin baiwa dukkanin mai hakki hakkinsa, kuma zalinci duffai ne ga ma'abotansa a ranar Alkiyama daga faruwar tsanani da tsorace-tsorace, kuma ya yi hani daga kwauro, da shi ne tsananin rowa tare da kwadayi, daga gareshi akwai takaitawa a bada hakkokin dukiya da tsananin kwadayi akan duniya, wannan nau'in na zalinci shi ne ya halakar da wanda suka gabacemu na al'ummai, ta inda ya ja su ga kashe sashinsu, da halarta abinda Allah Ya haramta na abubuwan haram.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung الولوف الأوكرانية الجورجية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bada dukiya da taimakawa 'yan uwa yana daga sabubban soyayya da sada (zumunci).
  2. Rowa da kwauro suna kaiwa zuwa ga sabo da alfasha da zunubai.
  3. Izina da halayen al'ummun da suka gabata.