عَنْ أَبِي الدَّرْدَاءِ رضي الله عنه: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«إِنَّ اللَّعَّانِينَ لَا يَكُونُونَ شُهَدَاءَ وَلَا شُفَعَاءَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2598]
المزيــد ...
Daga Abu Darda'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Lallai masu yawaita tsinuwa ba sa zama masu shaida ko masu ceto a ranar alƙiyama".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2598]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda yake yawaita tsinuwa akan wanda bai cancanteta ba to shi ya cancanci uƙuba biyu: Ta farko: Ba zai zama mai shaida ba a ranar alƙiyama akan al'ummu na isarwar Manzanninsu ga saƙonni zuwa garesu, kuma ba za'a karɓi shaidarsa ba a duniya; dan fasiƙancinsa, kuma ba za'a azurta shi da shahada ba ita ce mutuwa a tafarkin Allah. Ta biyu: Ba zai yi ceto ba a ranar alƙiyama lokacin da muminai suke yin ceto ga 'yan uwansu waɗanda suka cancanci (shiga) wuta.