عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه:
أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يَقُولُ فِي سُجُودِهِ: «اللهُمَّ اغْفِرْ لِي ذَنْبِي كُلَّهُ دِقَّهُ، وَجِلَّهُ، وَأَوَّلَهُ وَآخِرَهُ وَعَلَانِيَتَهُ وَسِرَّهُ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 483]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -:
Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a cikin sujjadarsa: "Ya Allah Ka gafarta mini dukkan zunubaina, ƙanƙaninsa, da babbansa, na farkonsa da na ƙarshensa, na bayyanensa da na ɓoyensa".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 483]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana addu'a a cikin sujjadarsa sai ya ce: (Ya Allah Ka gafarta mini zunubina) da suturta shi, kuma Ka kareni nauyinsu; sai Ka yi rangwami Ka ƙetare ka kauda kai, (dukkansa), ka taimake ni: (ƙanƙaninsa) ƙaraminsa da ƙanƙaninsa, (da babbansa) babbansa da mai yawansa, (da na farkonsa) farkon zunubi, (da na ƙarshensa), da abinda ke tsakaninsu, (na zahirinsa da na baɗininsa) daga abinda babu wani wanda ya sanshi sai Kai - tsarki ya tabbatar maKa -.