+ -

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المؤْمِنينَ رَضِيَ اللهُ عَنْهَا:
كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَجْتَهِدُ فِي الْعَشْرِ الْأَوَاخِرِ مَا لَا يَجْتَهِدُ فِي غَيْرِهِ.

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 1175]
المزيــد ...

Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita -:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana ƙoƙari a cikin goman ƙarshe irin ƙoƙarin da ba ya yi a cikin waninsa.

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1175]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan goman ƙarshe ya zo na Ramadan yana ƙoƙari a cikinsu da yin ibada da ɗa'a, kuma yana kai matuƙa a cikin nau'ikan alherai da sinfofin ayyukan kirki da ibadu mafi yawa daga abinda yake ƙoƙari a cikin waninsa; hakan dan girma da falalar waɗancan dararen da kuma dan neman daren Lailatul Ƙadr.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Yaran Tailand bushtu Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية النيبالية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwaɗaitarwa akan yawaita alheri da fuskokin ayyukan ɗa'a a cikin watan Ramadan a hade da kuma goman ƙarshe daga gare shi a keɓance.
  2. Goman ƙarshe na Ramadan suna farawa ne daga daren ashirin da ɗaya har zuwa ƙarshen wata.
  3. An so ribatar lokuta mafifita da ayyukan ɗa'a.