عَن أَبي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«الْحَلِفُ مَنْفَقَةٌ لِلسِّلْعَةِ، مَمْحَقَةٌ لِلرِّبْحِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 1606]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
"Rantsuwa mai sa anfani ce a haja (kayan sayarwa), kuma mai shafe albarkar riba ce".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1606]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi akan rantsuwa da kuma yawaita ta koda ta kasance akan gaskiya ne a siye da siyarwarsa, kuma ya bada labarin cewa ita sababi ce ta yawaitar haja da kaya da kuma samun ribarsu, sai dai hakan tawaya ce kuma ɓata albarkar riba ce da kuma kasuwanci, Allah - Maɗaukakin sarki - Zai iya dora wasu abubuwa da zasu ɓata su kodai ta hanyar sata ko gobara ko dilmiya a ruwa ko ƙwace ko fizge ko wasu abubuwa masu bijirowa daban waɗanda dukiyarsa zata lalace saboda su.