عَنْ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما قَالَ:
قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ غَدَاةَ الْعَقَبَةِ وَهُوَ عَلَى نَاقَتِهِ: «الْقُطْ لِي حَصًى» فَلَقَطْتُ لَهُ سَبْعَ حَصَيَاتٍ، هُنَّ حَصَى الْخَذْفِ، فَجَعَلَ يَنْفُضُهُنَّ فِي كَفِّهِ وَيَقُولُ: «أَمْثَالَ هَؤُلَاءِ فَارْمُوا» ثُمَّ قَالَ: «أَيُّهَا النَّاسُ، إِيَّاكُمْ وَالْغُلُوَّ فِي الدِّينِ، فَإِنَّما أَهْلَكَ مَنْ كَانَ قَبْلَكُمْ الْغُلُوُّ فِي الدِّينِ».
[صحيح] - [رواه ابن ماجه والنسائي وأحمد] - [سنن ابن ماجه: 3029]
المزيــد ...
Daga Abdullahi Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce a washegarin jifan babban shaidan alhali shi yana kan taguwarsa: "Ka tsintomin tsakwankwani". sai na tsinto masa tsakwankwani bakwai, su tsakwankwani ne na harbi, sai ya fara yana motsasu a tafinsa yana cewa: "Misalan wadananan sai ku yi jifa (da su)”. sannan ya ce: "Yaku mutane na haneku da wuce gona da iri a addini, kadai wuce gona da iri a addini shi ya halaka wadanda ke gabanku".
[Ingantacce ne] - - [سنن ابن ماجه - 3029]
Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - yana bada labarin cewa shi ya kasance tare da Annabi - tsira da amincin Alah su tabbata agare shi - a ranar babbar sallah wayewar garin jifan babban Shaidan a hajjin bankwana, sai ya umarce shi ya tsinto masa tsakwankwanin jifa, sai ya tsinto masa tsakwankwani bakwai, kowacce daya daga cikinsu ta kai girman wake ko bunduq, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -ya sanya su a hannu sa, sannan ya motsa su, ya ce: Ku yi jifa da kwatankwacin wannan a girma, sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargadar daga wuce gona da iri da tsanantawa da ketare iyaka a al'amuran addini, kadai ketare iyaka da wuce gona da iri da tsanantawa a addini shi ya halaka al'ammomin da suka gabata.