عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الخُدْرِيِّ رضي الله عنه أَنَّهُ سَمِعَ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«إِذَا رَأَى أَحَدُكُمُ الرُّؤْيَا يُحِبُّهَا فَإِنَّهَا مِنَ اللَّهِ، فَلْيَحْمَدِ اللَّهَ عَلَيْهَا وَلْيُحَدِّثْ بِهَا، وَإِذَا رَأَى غَيْرَ ذَلِكَ مِمَّا يَكْرَهُ، فَإِنَّمَا هِيَ مِنَ الشَّيْطَانِ، فَلْيَسْتَعِذْ مِنْ شَرِّهَا، وَلاَ يَذْكُرْهَا لِأَحَدٍ، فَإِنَّهَا لَنْ تَضُرَّهُ».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 7045]
المزيــد ...
Daga Abu Sa'id Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
"Idan ɗayanku ya ga wani abu a mafarkinsa da yake son sa to shi daga Allah ne, sai ya godewa Allah a kansa kuma ya bada labarin shi, idan kuma ya ga wanin hakan daga abinda yake ƙi, to kawai shi daga Shaiɗan ne, to sai ya nemi tsari daga sharrinsa, kuma kada ya fadawa kowa, to shi (mafarkin) ba zai cutar da shi ba".
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 7045]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa kyakkyawan mafarki mai faranta rai a cikin mafarki to daga Allah ne, kuma ya nunar da cewa ya godewa Allah akansa, ya kuma bada labarinsa, idan kuma ya ga abinda yake ƙinsa yake baƙanta masa rai to shi kawai daga Shaiɗan ne; to ya nemi tsarin Allah daga sharrinsa, kada ya faɗawa kowa; (to mafarkin) ba zai cutar da shi ba , inda Allah Ya sanya abinda aka ambata sababi na kuɓuta daga abinda yake na mugun mafarkin .