+ -

عَنْ ثَوْبَانَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«أَفْضَلُ دِينَارٍ يُنْفِقُهُ الرَّجُلُ، دِينَارٌ يُنْفِقُهُ عَلَى عِيَالِهِ، وَدِينَارٌ يُنْفِقُهُ الرَّجُلُ عَلَى دَابَّتِهِ فِي سَبِيلِ اللهِ، وَدِينَارٌ يُنْفِقُهُ عَلَى أَصْحَابِهِ فِي سَبِيلِ اللهِ» قَالَ أَبُو قِلَابَةَ: وَبَدَأَ بِالْعِيَالِ، ثُمَّ قَالَ أَبُو قِلَابَةَ: وَأَيُّ رَجُلٍ أَعْظَمُ أَجْرًا مِنْ رَجُلٍ يُنْفِقُ عَلَى عِيَالٍ صِغَارٍ، يُعِفُّهُمْ أَوْ يَنْفَعُهُمُ اللهُ بِهِ وَيُغْنِيهِمْ.

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 994]
المزيــد ...

Daga Sauban - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Mafificin dinaren (kudi) da mutum zai ciyar da shi: Dinarin da ya ciyar da shi ga iyalansa, da dinaren da mutum yake ciyar da shi ga dabbarsa a tafarkin Allah, da dinaren da yake ciyar da shi ga abokansa a tafarkin Allah" Abu Kilaba ya ce: "Sai ya fara da iyali, sannan Abu Kilaba ya ce: Kuma wanne mutum ne mafi girman lada kamar mutumin da yake ciyar da iyali ƙanana don ya rufa musu asiri ko Allah Ya anfanar da su da shi, kuma ya wadata su".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 994]

Bayani

(Annabi) tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi ya bayyana wasu Nau’uka a cikin ciyarwa, ya kuma jerantasu idan fuskokin ciyarwar sun gagara gwargwadan mafi wajabci akanka, sai ya fara da mafi muhimmanci sai mafi muhimmanci; sai ya sanar da cewa mafi yawan dukiya a lada ita ce wadda musulmi yake ciyar da ita ga wanda ciyarwarsa ta wajaba akan shi; kamar mata da ɗa, sannan ciyarwa ga abin hawa wanda aka tanada dan yaƙi a tafarkin Allah, sannan ciyarwa ga abokansa da ayarinsa a halin kasancewarsu mayaƙa a tafarkin Allah.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Jeranta ciyarwa a falala ta fuskar da aka ambata, sai a lura da hakan a lokacin da suka taru.
  2. Bayanin cancantar ciyarwa ga iyali a falala akan wasunsu.
  3. Ciyarwa a yaƙi saboda Allah tana daga mafi girman ciyarwa, kamar tanadar kaya da mayaka a Jihadi.
  4. An ce: Abin nufi da tafarkin Allah dukkanin aikin ɗa'a kamar aikin hajji a misali.