+ -

عن أبي سعيد الخدري رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«الحَسَن والحُسَيْن سَيِّدا شَباب أهْل الجنة».

[صحيح] - [رواه الترمذي وأحمد] - [سنن الترمذي: 3768]
المزيــد ...

Daga Abu Sa'idu Khudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Alhasan da Alhusain su ne shugabannin matasan 'yan Aljanna".

[Ingantacce ne] - - [سنن الترمذي - 3768]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa jikokinsa biyu Alhassan da Alhussain 'ya'yan Ali ɗan Abu Ɗalib da Faɗima 'yar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma Allah Ya yarda da su -, su ne shugabannin wanda ya mutu a falala alhali shi yana saurayi kuma ya shiga aljanna, ko cewa sune shugabannin matasan 'yan aljanna in an cere Annabawa da Khalifofi Masu shiryarwa.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassara Yaren Faransanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Yaran Tailand bushtu Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية النيبالية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. A cikinsa akwai falala ta zahiri ga Hassan da Hussain - Allah Ya yarda da su -.
  2. An ce a cikin ma'anar hadisin: Cewa su a lokacin hadisin sune shugabannin waɗanda sune daga 'yan aljanna cikin matasan wannan zamanin, ko kuma cewa sune mafifita daga waɗanda falala mai gamewa ba ta tabbata a cikinsa ba kamar Annabawa da Khalifofi, ko kuma cewa sune shugabannin waɗanda suka siffantu da siffofin samartaka da yarinta kamar karamci da gwarzantaka, kuma bai zo da shekarun matasa da hakan ba; domin Hassan da Hussain sun mutu alhali suna gwaraza.