+ -

عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرِو بْنِ الْعَاصِ رضي الله عنهما أنَّ رَسولَ اللَّهِ صلَّى اللَّهُ عليْه وسلَّمَ، قال:
«قَدْ أَفْلَحَ مَن أَسْلَمَ، وَرُزِقَ كَفَافًا، وَقَنَّعَهُ اللَّهُ بما آتَاهُ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 1054]
المزيــد ...

Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Aas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Haƙiƙa wanda ya miƙa wuya (ga Ubangijinsa), kuma aka azurta shi da abu kaɗan (gwargwadan buƙatarsa), kuma Allah Ya wadata shi da abin da Ya ba shi to ya rabauta».

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1054]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa haƙiƙa ya rabauta wanda ya miƙa wuya ga Ubangijinsa sai aka shiryar da shi kuma aka datar da shi ga Musulunci, kuma aka azirta shi gwagwadan buƙatarsa daga halal ba tare da ƙari ko ragi ba, kuma Allah Ya sanya shi mai yarda da abinda Ya bashi.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Swahili Yaran Tailand Asami الأمهرية الهولندية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwanciyar hankalin mutum yana cikin cikar Addininsa da isuwar abin cinsa da kuma wadatuwarsa da abinda Allah Ya ba shi.
  2. Kwaɗaitarwa a kan wadatuwa da abinda aka baka na duniya tare da Musulunci da kuma sunnah.