عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضيَ اللهُ عنهما أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يَقُولُ:
«اللهُمَّ لَكَ أَسْلَمْتُ، وَبِكَ آمَنْتُ، وَعَلَيْكَ تَوَكَّلْتُ، وَإِلَيْكَ أَنَبْتُ، وَبِكَ خَاصَمْتُ، اللهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِعِزَّتِكَ، لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ أَنْ تُضِلَّنِي، أَنْتَ الْحَيُّ الَّذِي لَا يَمُوتُ، وَالْجِنُّ وَالْإِنْسُ يَمُوتُونَ».
[صحيح] - [متفق عليه، وهذا لفظ مسلم ورواه البخاري مختصرًا] - [صحيح مسلم: 2717]
المزيــد ...
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana cewa:
"Ya Allah gareKa na miƙa wuya, kuma da Kai ne na yi imani, gareka ne na dogara, gareKa ne na dawo, saboda Kai ne na yi husuma, Ya Allah lallai ni ina neman tsari da buwayarKa, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai (kada) Ka ɓatar da ni, Kaine Rayayye wanda ba zai mutu ba, aljanu da mutane kuwa zasu mutu"
[Ingantacce ne] - - [صحيح مسلم - 2717]
Ya kasance daga addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kasance yana cewa: (Ya Allah gareKa ne na miƙa wuya) kuma na jawu, (da Kai ne na yi imani) na gasgata kuma na yi iƙrari, (kuma gareKa ne na dogara) na fawwala na kuma dogara, (gareKa ne na koma) na koma na fuskanta, (saboda Kai ne na yi husuma) na yi jayayya da maƙiyanKa, (Ya Allah ni ina neman tsarinKa) ina fakewa (da buwayarKa) da hanawarKa da kuma rinjayenKa, (babu abin bautawa da gaskiya sai Kai) kuma babu wani abin bautawa da gaskiya inba Kai ba, (da Ka ɓatar da ni) daga shiriya da dacewa da yardarKa, (Kai ne Rayayye wanda ba zai mutu ba) kuma ba zai ƙareba, (aljanu da mutane kuwa zasu mutu).