عَن عَبْدِ اللهِ بْنِ عَمْرِو بْنِ الْعَاصِ رضي الله عنهما أَنَّهُ سَمِعَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، يَقُولُ:
«إِنَّ قُلُوبَ بَنِي آدَمَ كُلَّهَا بَيْنَ إِصْبَعَيْنِ مِنْ أَصَابِعِ الرَّحْمَنِ، كَقَلْبٍ وَاحِدٍ، يُصَرِّفُهُ حَيْثُ يَشَاءُ» ثُمَّ قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «اللهُمَّ مُصَرِّفَ الْقُلُوبِ صَرِّفْ قُلُوبَنَا عَلَى طَاعَتِكَ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2654]
المزيــد ...
Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Aas - Allah Ya yarda da su - cewa shi ya ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
"Lallai cewa zukatan 'ya'yan Adam dukkansu (suna) tsakanin yatsu biyu daga yatsun (Ubangiji) al-Rahman, kamar zuciya ɗaya, yana jujjuyata yadda Ya so" sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Ya Allah Ya mai jujjuya zukata Ka juya zukatanmu a kan biyayyarKa".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2654]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa zukatan 'ya'yan Adam dukkansu suna tsakanin yatsu biyu daga yatsun (Ubangijin) shi ne al-Rahman kamar zuciya ɗaya; Yana juya ta yadda Ya so; idan Ya so Ya tsayar da ita akan gaskiya, idan kuma Ya ga dama ya karkatar da ita daga gaskiya, kuma jujjuyawarSa a cikin dukkannin zukata kamar tasarrufi ne a abu ɗaya, wani sha'ani ba ya shagaltar da Shi - tsarki ya tabbatar maSa - daga wani sha'anin, sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi adu'a sai ya ce: Ya Allah ya Mai jujjuya zukata wani lokaci zuwa ga ɗa'a, wani lokaci kuma zuwa saɓo, wani lokaci kuma zuwa tinawa wani lokaci kuma zuwa rafkana, ka juyar da zukatanmu akan biyayyarKa.