عن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما : «أن تَلْبِيَةَ رسول الله صلى الله عليه وسلم : لَبَّيْكَ اللهم لَبَّيْكَ، لبيك لا شريك لك لبيك، إن الحمد والنعمة لك والملك، لا شريك لك». قال: وكان عبد الله بن عمر يزيد فيها: «لَبَّيْكَ لَبَّيْكَ وَسَعْدَيْكَ، والخير بيديك، وَالرَّغْبَاءُ إليك والعمل».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Abdullahi Dan Umar - Allah ya yarda da su - " cewa Talbiyar Manzon Allah -- Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi - "Amsawarka Amsawa ya Ubangiji, Amsawarka ya Ubangiji baka da Abokin tarayya Amsawarka, lallai cewa godiya taka ce kuma ni'ama ma taka ce kuma Mulkin ma naka ne baka da Abokin tarayya."
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Abdullahi Dan Umar - Allah ya yarda da shi - yana bamu bayani cewa yadda Talbiyyar Annabi -Tsira da Amincin Allah da amincin Allah su tabbata a gareshi a cikin Hajji da Umra, "Amsawarka Amsawa ya Ubangiji, Amsawarka ya Ubangiji baka da Abokin tarayya Amsawarka, lallai cewa godiya taka ce kuma ni'ama ma taka ce kuma Mulkin ma naka ne baka da Abokin tarayya" kuma shelantawa ne da amsawa Allah Madaukaki cikin kiran da yayi zuwa Hajjatar Dakinsa , Amsawa bayan amsawa da kuma tsarkake niyya gare shi, da kuma fuskantarsa, da kuma furuci da godiya da godiyarsa , da Ni'amarsa , da kuma kadaita shi cikin hakan da kuma Mulkin baki dayan Halittu babu abokin tarayya a gare shi cikin haka baki daya, kuma Dan Umar - Allah ya yarda da shi - yana karawa cikin abunda wannan Talbiyya ta kunsa , sabida karfafawa ta yadda ya kara wata Talbiyya da ta kunshi Amsawarka Allah kuma rabauta yana wurinka , kuma dukkan Alkairi yana Hannnunka kuma Bukatuwa zuwa gareka ake kaita da kuma aiki, to kunga Karshen aiki zuwa ga Allah Madaukaki ya ke tabbat Niyya da kuma neman lada.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin