عن جابرٍ رضي الله عنه قال: قدِمنا مع رسولِ الله صلى الله عليه وسلم ، ونحنُ نقولُ: لبيك بالحجِّ، فأمرَنا رسولُ الله صلى الله عليه وسلم فجعلناها عُمرةً.
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Jabir -Allah ya yarda da shi- ya ce Mun iso tare da Manzon Allah -Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- kuma mu muna cewa Amsarka Hajji, Sai Manzon Allah -Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- ya Umarce mu sanya ta Umra.
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Jabir yana bamu bamu labari -Allah ya yarda da shi cewa sun iso tare da Manzon Allah -Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- a Hajjin bankwana mafi yawansu kuma suna cewa: "Amsawarka aikin Hajji" ai suna cewa sunyi Ifradin Hajji to sai Annabi -Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- ya Umarci wanda duk bai tanadi Hadaya daga cikin su, kan ya warware Hajjinsa zuwa Umra; don su koma masu Hajjin Tamattu'i, sai suka yi hakan- Allah ya yarda da su.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Uighur Portuguese
Manufofin Fassarorin