عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قال: قال رَسُولُ الله صلى الله عليه وسلم:
«إِنَّ اللهَ يَغَارُ، وَإِنَّ الْمُؤْمِنَ يَغَارُ، وَغَيْرَةُ اللهِ أَنْ يَأْتِيَ الْمُؤْمِنُ مَا حَرَّمَ عَلَيْهِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 2761]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Lallai Allah Yana kishi, muminima yana kishi, kishin Allah (shi ne) mumini ya zo wa abinda (Allah) ya haramta masa".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2761]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah Yana kishi kuma Yana ki, kamar yadda cewa mumini yana kishi yana kuma ki, kuma cewa sababin kishin Allah shi ne mumini ya zo wa abinda Allah Ya haramta akansa na alfasha kamar ; zina da liwadi da sata da shan giya da wasunsu na alfasha.