عن أبي عبد الله الجَدَلِي قال: سألتُ عائشة رضي الله عنها ، عن خُلُق رسول الله صلى الله عليه وسلم فقالت: «لم يكن فاحِشًا ولا مُتَفَحِّشًا ولا صَخَّابًا في الأسواق، ولا يَجْزي بالسيئةِ السيئةَ، ولكن يَعْفو ويَصْفَح».
[صحيح] - [رواه الترمذي وأحمد]
المزيــد ...
Daga Abu Abdullahi Al-jadali ya ce: na tambayi Nana Aisha game da halayen Manzon Allah SAW sai ta ce: "Bai kasance Mai Mummunar Magana ba ko Mai Mai yawan yin Mummunar Maganar, ko mai kwararoto a Kasuwa, kuma baya rama Mummuna da mummuna, Kuma shi yana yin Afuwa ya kuma kau da kai"
[Ingantacce ne] - [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi]
Abu Abdullahi Al-jadali ya tambayi Nana Aisha game da halayen Manzon Allah SAW sai ta bashi labarin cewa shi mai Manyan Halaye Bai kasance Mai Mummunar Magana ba ko Mai Mai yawan yin Mummunar Maganar, ko mai kwararoto a Kasuwa saboda mummunan halinsa, kuma baya rama Mummuna da mummuna, Kuma shi yana yin Afuwa ya kuma kau da kai