عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّهُ سَمِعَ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«أَرَأَيْتُمْ لَوْ أَنَّ نَهَرًا بِبَابِ أَحَدِكُمْ يَغْتَسِلُ فِيهِ كُلَّ يَوْمٍ خَمْسًا، مَا تَقُولُ ذَلِكَ يُبْقِي مِنْ دَرَنِهِ؟» قَالُوا: لَا يُبْقِي مِنْ دَرَنِهِ شَيْئًا، قَالَ: «فَذَلِكَ مِثْلُ الصَّلَوَاتِ الخَمْسِ، يَمْحُو اللَّهُ بِهِ الخَطَايَا».  
                        
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 528]
                        
 المزيــد ... 
                    
Daga Abu Huraira Allah ya yarda da shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
"Shin kuna ganin cewa da ace akwai wata korama a kofar dayanku yana wanka a cikinta kowacce  rana sau biyar, shin kuna zatan wani abu na dattinsa zai rage ?" Suka ce: Ba abin da zai rage dattinsa, ya ce: "To hakan tamkar salloli biyar ne, Allah Yana shafe kurakurai da su". 
                                                     
                                                                                                    
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 528]                                            
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kamanta salloli biyar a kowanne yini da dare a kawarwa da kankarewarsu ga kananan zunubai da kurakurai da korama a kofar mutum da yake wanka a cikinta kowacce rana sau biyar, babu wani abu da zai ragu daga dattinsa.