عن عمار بن ياسر رضي الله عنهما قال: «بَعَثَنِي النبي صلى الله عليه وسلم في حَاجَة، فَأَجْنَبْتُ، فَلَم أَجِد المَاءِ، فَتَمَرَّغْتُ فِي الصَّعِيدِ، كَمَا تَمَرَّغ الدَّابَّةُ، ثم أَتَيتُ النبي صلى الله عليه وسلم فَذَكَرتُ ذلك له، فقال: إِنَّمَا يَكْفِيك أن تَقُولَ بِيَدَيكَ هَكَذَا: ثُمَّ ضَرَب بِيَدَيهِ الأَرْضَ ضَرْبَةً وَاحِدَةً، ثُمَّ مَسَحَ الشِّمَالَ عَلَى اليَمِينِ، وظَاهِرَ كَفَّيهِ وَوَجهَهُ».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Dag Ammar Dan Yasir -Allah ya yarda da shi- yace:"Annabi -tsira da amincin Allah ya aika ni,sai janaba ta same ni,ban sami ruwa ba,sai nayi birgima a turbaya,kamar yadda dabba ke yi,sannan naje wajen Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi-sai na fada masa,sai yace:"Kayi haka da hannunka kadai ya isarma-sai ya bugi kasa da hannunsa sau daya,sannan ya shafa hagunsa a kan damansa,ya kuma shafi bayan tafukansa da fuskarsa".
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Annabi -tsira da amincin Allah- ya aiki Ammar Dan Yasir kan wata bukata,sai janaba ta same shi, bai sami ruwan da zai yi wanka dashi ba,kuma ya kasance bai san hukuncin taimama ga mai janaba ba,ya san hukuncin taimama ga mai karamin kari ne.sai yayi tsammanin tunda ana yiwa karamin kari taimama,to babban kari kuma sai an game jiki da kasa,kamar yadda ake yin tsarki na ruwa,sai yayi ta birgima a kasa har ya game jikinsa da turbaya sannan yayi salla,sai yazowa Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yana rike da abin da yayi a ransa,don kuwa ya yi ne bisa kokarin kansa,sai ya fadawa Annabi abin da ya faru,don yaga ko yayi daidai ko a'a?sai Annabi tsira da amincin Allah yace: ka bugi kasa da hannayenka,bugu daya,sannan ka shafi damanka da hagunka,ka shafi bayan hannayenka da fuskarka,kamar taimamar alwala, ya isar maka daga game jikinka da turbaya

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الدرية
Manufofin Fassarorin