عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُمَا قَالَ:
كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَليهِ وَسَلَّمَ لا يَعْرِفُ فَصْلَ السُّورةِ حَتَّى تَنْزِلَ عَليْهِ {بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ}.
[صحيح] - [رواه أبو داود] - [سنن أبي داود: 788]
المزيــد ...
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce:
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance ba ya sanin rabewar sura har sai {Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai} ta sauka a gare shi.
[Ingantacce ne] - [Abu Daud Ya Rawaito shi] - [سنن أبي داود - 788]
Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - yana bayyana cewa surorin Alkur’ani sun kasance suna sauka ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - amma ba ya sanin rabewarsu da karewarsu har sai {Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai} ta sauka gareshi, sai ya san cewa surar da ta gabata an cikata, kuma cewa ita farko ce ga sabuwar sura.