عن عبادة بن الصامت رضي الله عنه ، قال: «كان نبيُّ اللهِ صلى الله عليه وسلم إذا أُنْزِلَ عليه الوحيُ كُرِبَ لذلك وتَرَبَّدَ وجهُه».
[صحيح] - [رواه مسلم]
المزيــد ...
Daga Ubada Bn Samit -Allah yarda da shi- ya ce: "Annabin Allah SAW ya kasance idan an saukar Masa da Wahayi yakan shiga qunci fuskarsa ta turvune"
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance a kansa lokacin da wahayi ya sauka a gare shi, zai kasance cikin kunci da damuwa game da hakan kuma fuskarsa za ta canza. Saboda nauyin wahayi da wahalar samu, sai ya - Allah ya kara masa yarda - ya fi kulawa da lamarin wahayi, kuma ya ji tsoron hakkin da yake nema na bauta da godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya daukaka umurnin Allah Madaukakin Sarki da kwarewarsa.