+ -

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنينَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا أَنَّهَا قَالَتْ:
مَا خُيِّرَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بَيْنَ أَمْرَيْنِ إِلَّا أَخَذَ أَيْسَرَهُمَا، مَا لَمْ يَكُنْ إِثْمًا، فَإِنْ كَانَ إِثْمًا كَانَ أَبْعَدَ النَّاسِ مِنْهُ، وَمَا انْتَقَمَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لِنَفْسِهِ إِلَّا أَنْ تُنْتَهَكَ حُرْمَةُ اللَّهِ، فَيَنْتَقِمَ لِلَّهِ بِهَا.

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 3560]
المزيــد ...

Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - cewa ita ta ce:
Ba'a taɓa ba wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - zabi ba tsakanin abubuwa biyu face sai ya zaɓi mafi sauƙinsu, matuƙar bai kasance saɓo ba, idan ya kasance saɓo ne to ya kasance ya fi kowa nisantar shi, kuma Annabi bai bai taɓa ramuwar gayya ga kansa ba ko sau ɗaya, sai dai idan an keta hurumin Allah, sai ya yi hukunci saboda Allah da ita.

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 3560]

Bayani

Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labari game da wasu daga ɗabi'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, daga abinda ta ambata: Cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba'a taɓa ba shi zaɓi ba tsakanin al'amura biyu sai ya ɗauki mafi sauƙinsu muddin dai mafi sauƙin ba mai kaiwa zuwa zunubi ba ne, to cewa shi zai kasance mafi nisantar mutane ga wannan zunubin kuma zai zaɓi mafi tsanani a lokacin. Kuma (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi bai taɓa ramuwa ba ga kansa a keɓance ba, kai ya kasance yana kau da kai kuma yana afuwa daga haƙƙinsa sai dai idan keta alfarmomin Allah aka yi sai ya zama ya yi hukunci saboda Allah, kuma ya kasance mafi tsananin mutane a fushi saboda Allah.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الصربية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. An so riƙo da sauƙi a cikin al'amura matuƙar dai babu saɓo a cikinsa.
  2. Sauƙin Musulunci.
  3. Halaccin fushi saboda Allah - Maɗaukakin sarki -.
  4. Abinda (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yake akansa na juriya da haƙuri da tsayuwa da haƙƙi a cikin tsaida iyakokin Allah - Maɗaukakin sarki -.
  5. Ibnu Hajar ya ce: A cikinsa akwai barin riƙo da abu mai wahala, da wadatuwa da sassauƙa, da barin nacewa a cikin abinda ba'a buƙatuwa zuwa gare shi .
  6. Kwaɗaitarwa akan afuwa sai dai a cikin haƙƙoƙin Allah - Maɗaukakin sarki -.