عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ مَسْعُودٍ رَضيَ اللهُ عنهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهُ كَانَ يَقُولُ:
«اللهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْهُدَى وَالتُّقَى، وَالْعَفَافَ وَالْغِنَى».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2721]
المزيــد ...
Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kasance yana cewa:
«Ya Ubangiji ina roƙonKa shiriya da tsoron Allah, da kamewa, da wadata».
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2721]
Ya kasance daga addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: «Ya Allah ni ina roƙonKa shiriya» hanya madaidaiciya na sanin gaskiya da aiki da ita. «Da tsoron Allah», ruko da umarni da nisantar hane-hane. «Da kamewa» kamewa daga abinda ba ya halatta kuma ba shi da kyau na magana ne ko aiki. «Da wadatuwa» daga halitta, inda ba zai yi buƙatuwa ba zuwa ga wani inba Uabngijinsa - Mai girma da ɗaukaka ba -.