+ -

عَنْ بُرَيْدَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«مَنْ حَلَفَ بِالْأَمَانَةِ فَلَيْسَ مِنَّا».

[صحيح] - [رواه أبو داود وأحمد] - [سنن أبي داود: 3253]
المزيــد ...

Daga Buraidah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce -:
"Wanda ya rantse da amana to baya daga cikinmu".

[Ingantacce ne] - - [سنن أبي داود - 3253]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani kuma ya gargaɗar daga rantsuwa da amana, kuma cewa wanda ya aikata hakan to ba shi daga cikinmu.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Yaran Tailand bushtu Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Haramcin rantsuwa da wanin Allah - Maɗaukakin sarki -, kuma daga cikin hakan: amana, kuma hakan yana daga ƙaramar shirka.
  2. Amana ta ƙunshi ɗa'a da bauta da ajiya da bayarwa hannu da hannu da amintarwa.
  3. Rantsuwa bata ƙulluwa sai da Allah - Maɗaukakin sarki - ko da wani suna daga sunayenSa ko wata siffa daga siffofinSa.
  4. AlKhaɗɗabi ya ce: Wannan yana kama da karhancin ya zama saboda cewa shi ya yi umarni a yi rantsuwa da Allah ne da kuma siffofinSa, amana kuwa ba ta daga siffofinSa, kawai ita wani al'amari ce daga aumarninSa, kuma farilla ce daga farillanSa, sai aka hanasu su rantse da ita dan abinda ke cikin hakan na daidaitawa tsakaninta da tsakanin sunayen Allah - Mai girma da ɗaukaka - da kuma siffofinSa.