عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: مَا خَطَبَنَا نَبِيُّ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِلَّا قَالَ:
«لَا إِيمَانَ لِمَنْ لَا أَمَانَةَ لَهُ، وَلَا دِينَ لِمَنْ لَا عَهْدَ لَهُ».
[حسن لغيره] - [رواه أحمد] - [مسند أحمد: 12383]
المزيــد ...
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai taɓayi mana wata huɗuba ba sai ya ce:
«Babu imani ga wanda ba shi da amana, kuma babu Addini ga wanda ba shi da alƙawari».
[Hasan ne ta wani Sanadin] - [Ahmad ne ya rawaito shi] - [مسند أحمد - 12383]
Anas ɗan malik - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa da wahala Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi huɗuba ko ya yi wa'azi sai ya ambaci al'amura biyu: Na farko: Babu imani cikakke ga wanda a ransa akwai ha'inci ga wani mutum a cikin dukiyarsa ko ransa ko kuma iyalansa. Na biyu: Babu Addini cikakke ga wanda yake ha'intar alƙawurra kuma yake warwaresu.