Karkasawa:
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:

«كُلُّ أُمَّتِي مُعَافًى إِلَّا المُجَاهِرِينَ، وَإِنَّ مِنَ المُجَاهَرَةِ أَنْ يَعْمَلَ الرَّجُلُ بِاللَّيْلِ عَمَلًا، ثُمَّ يُصْبِحَ وَقَدْ سَتَرَهُ اللَّهُ عَلَيْهِ، فَيَقُولَ: يَا فُلاَنُ، عَمِلْتُ البَارِحَةَ كَذَا وَكَذَا، وَقَدْ بَاتَ يَسْتُرُهُ رَبُّهُ، وَيُصْبِحُ يَكْشِفُ سِتْرَ اللَّهِ عَنْهُ».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
"Duk al'ummata an yafe musu sai masu bayyanarwa, kuma yana daga bayyanarwa mutum ya aikata wani aiki (mummuna) da daddare, sannan ya wayi gari Allah Ya rufa masa asiri, sai ya ce: Ya (ya falalarsa kansa) wane, jiya da daddare na aikata kaza da kaza, alhali ya kwana Uabangijinsa Ya rufa masa asiri, shi kuma ya wayi gari yana tona asirin da Allah Ya rufa masa".

Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa musulmi mai laifi ana yi masa kwadayin afuwar Allah da gafararSa, sai mai bayyanar da sabo dan alfahari da rashin kunya, to ba ya cancantar afuwa; ta inda yake aikata laifi da daddare, sannan ya wayi gari alhali Allah Ya rufa masa asiri, sai ya zantar da waninsa da cewa shi ya aikata sabo kaza jiya, ya kwana Ubangijinsa Ya rufa masa asiri, shi kuma ya wayi gari yana tona asirin da Allah Ya rufa masa!!

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Yaran Tamili bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الدرية
Manufofin Fassarorin

Ma"anonin Kalmomi

الملاحظة
المجاهرون: المعلنون بالمعاصي المتحدثون بها على سبيل التفاخر.
من يدخن في الشارع دون فخر بالمعصيه هل من المجاهره
النص المقترح لا يوجد...

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Munin bayyanar da sabo bayan rufa asirin Allah - Madaukakin sarki - ya yi a gare shi .
  2. A bayyanar da sabo akwai yayata alfasha tsakanin muminai.
  3. Wanda Allah Ya rufa masa asiri a duniya Zai rufa masa asiri a lahira, wannan yana daga yalwar rahamar Allah - Madaukakin sarki - ga bayinSa.
  4. Wanda aka jarraba da wani sabo to ya wajaba ya rufawa kansa asiri kuma ya tubarwa Allah.
  5. Girman zunubin masu bayyanarwa wadanda suke nufin bayyanar da sabo, kuma suna barin afuwar Allah taba wuce su.
kashe kashe
Kari